Pars Today
Ministocin harkokin wajen kasashen Amurka dana Koriya ta Kudu, sun sanar da soke atisayen sojin hadin guiwa na tsakanin kasashen da aka shirya yi a watan Disamba mai zuwa.
Gwamnatin kasar Amurka ta bude sansanin sojojinta mafi girma a duniya a kasar Korea ta kudu a dai dai lokacinda ba'a da de kammala taron shugaba Trump da tokoransa na Korea ta Arewa Kim Jong un ba.
Shugaba Donald Trump, na Amurka ya bayyana cewa, mai yiwa a daga ganawar da ya shirya zai yi da takwaransa na Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, a ranar 12 ga watan Yuni a Singapore
Shugaban Amurka Donald Trump, zai karbi bakuncin takwaransa na Koriya ta kudu Moon Jae-in a ranar 22 ga wannan watan, gabanin ganawar da aka shirya yi tsakaninsa da Shugaban Koriya ta arewa kim Jong Un.
Koriya ta Kudu ta ce Shugaba Kim Jong-un na Koriya ta Arewa ya shaida cewa a watan Mayu mai kamawa zai rufe cibiyar da kasarsa take amfani da ita wajen gwajin makaman nukiliya.
Shugaba Kim Jong Un, na Koriya ta Arewa ya isa koriya ta kudu a wata ziyara irin ta ta farko mai manufar shafe fagen tattaunawar zaman lafiya ta tsakanin kasashen biyu.
Kasashen duniya da dama sun yi maraba da shirin ganawar ba-zata da shugaba Kim Jong-Un, na Koriya ta Arewa ya yi wa Donald Trump na Amurka.
Koriya ta arewa ta sanar da cewa tana iya yin watsi da shirinta na ci gaba da kera makaman nukiliya matukar dai ta samu lamuni mai karfi da zai tabbatar mata da tsaronta.
Wata kotu a Koriya ta Kudu, ta bukaci daurin shekaru 30 ga tsohuwar shugabar kasar, Park Geun-hye, da take fuskantar tuhuma kan cin hanci da rashawa.
Shugaban Koriya ta Kudu, Moon Jae-in, ya bukaci Amurka da ta sassauta bukatunta don samun tattaunawa da mahukuntan Pyongyang.