Pars Today
Mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta kasar Masar, Mohamed al-Shenawy, ya fi karbar kyautar dan wasan da ya fi taka leda “Man of the Match” da aka ba shi a wasan da suka buga da kasar Uruguay bayan da ya fahimci cewa kamfanin giyan nan na Budweiser ne ya dauki nauyin ba da kyautar.
A ci gaba da gasar kwallon kafa ta duniya dake gudana yanzu haka da kasar Rasha, yau Lahadi an fafata tsakanin Costa Rica da Serbia, inda Saria ta doke Costa Rica da 1-0, a rukunin E
A ci gaba da gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a kasar Rasha, kungiyar kwallon kafa ta Iran ta sami nasara a kan kasar Moroko da ci daya da nema, a daya bangaren kuma kungiyar kwallon kafa ta kasar Uruguay ta sami nasara a kan kasar Masar ita ma da ci daya da nema.
Rasha dake karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya 2018, ta lallasa Saudiyya da ci 5 da 0 a wasan bude gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya da aka yi a birnin Mosko.
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, ta sanar da cewa hadin guiwar kasashen Amurka da Canada da kuma Mexico, a mastayin wadanda zasu karbi bakuncin gudadanar da gasar cin kofin duniya a shekara 2026.
Babban mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kasar Spain, Zinedine Zidane ya sanar da ajiye aikinsa a matsayin mai horar da kungiyar kasa da mako guda bayan da ya jagorancin kungiyar wajen lashe kofin zakaran zakarun Turai a karo na uku a jere.
Ministan wasanni da matasa na kasar Masar, Khalid Abd El-aziz, ya bayyana fatan cewa shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Mohammed Salah zai buga gasar kwallon kafa ta duniya da za gudanar a kasar Rasha duk kuwa da rauni da ya samu a kafadarsa a jiya Asabar.
Kungiyar kwallon kafa ta mata na cikin na cikin dakin wasa da aka fi sani da Futsal na Iran ta zama zakaran zakarun nahiyar Asiya bayan da ta lallasa takwararta na kasar Japan da ci 5-2.
Kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya Super Eagles ta sami nasarar kai wa ga gasar kusa da na karshe wato Semi-Finals a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake gudanarwa a kasar Moroko bayan da ta lallasa takwararta ta kasar Angola da ci 2-1 a karawar da suka yi a daren jiya Lahadi.
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta musanta labarin da wasu kafafen watsa labaran kasar suka watsa na cewa wasu mutane sun mutu sakamakon turmutsutsu da aka fuskanta a loakcin gasar kwallon kafa da kungiyar kwallon kafa ta Nijeriyan ta yi da takwararta ta kasar Zambiya a jiya Asabar a garin Uyo na jihar Akwa Ibom.