Zinedine Zidane Ya Sanar Da Kudurinsa Na Barin Kungiyar Real Madrid
(last modified Thu, 31 May 2018 16:00:26 GMT )
May 31, 2018 16:00 UTC
  • Zinedine Zidane Ya Sanar Da Kudurinsa Na Barin Kungiyar Real Madrid

Babban mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kasar Spain, Zinedine Zidane ya sanar da ajiye aikinsa a matsayin mai horar da kungiyar kasa da mako guda bayan da ya jagorancin kungiyar wajen lashe kofin zakaran zakarun Turai a karo na uku a jere.

Zinedine Zidane ya sanar da hakan ne a wani taron manema labarai na gaggawa da kungiyar ta kira a yau din nan Alhamis inda ya ce bisa radin kansa ne ya dauki wannan mataki sakamakon sauye-sauyen da aka samu kuma kulob din na bukatar wani sabon salo, don haka yayi fatan alheri wa kulob din wanda ya bayyana ta a matsayin kulob din da yake tsananin so.

Wannan sanarwar dai ta zo wa mutane musamman ma magoya bayan kungiyar ta Real Madrid a matsayin ba za ta ganin irin nasarorin da Zidane din ya samu, kamar yadda shi kansa shugaban kungiyar Florentino Perez ya bayyana mamakinsa da wannan mataki da Zidane din ya dauka.

Zidane dan shekaru 45 a duniya, ya zama kocin kungiyar ta Real Madrid ne a shekara ta 2016 inda tsawon wannan lokacin ya jagoranci kungiyar a wasanni 149 inda suka sami nasara a wasannin 104, kamar yadda kuma ya lashe kofuna har guda 9 da suka hada da kofin zakaran zakarun Turai guda 3, La Liga 1 da sauransu.

'Yan wasan kungiyar ta Real Madrid da sauran magoya bayanta suna ci gaba da nuna alhininsu dangane da wannan mataki na Zidane.