AFCONU20 : Nijar Ta Yi Canjaras Da Burundi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35108-afconu20_nijar_ta_yi_canjaras_da_burundi
A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na 'yan kasa da shekara 20, dake gudana a Jamhuriyar Nijar, tawagar kwallon kafa ta Nijar, ta yi canjaras da Burundi 3-3, a wasan da suka buga da yammacin jiya a babban filin kwallon kafa na Yamai.
(last modified 2019-02-06T10:27:26+00:00 )
Feb 06, 2019 10:27 UTC
  • AFCONU20 : Nijar Ta Yi Canjaras Da Burundi

A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na 'yan kasa da shekara 20, dake gudana a Jamhuriyar Nijar, tawagar kwallon kafa ta Nijar, ta yi canjaras da Burundi 3-3, a wasan da suka buga da yammacin jiya a babban filin kwallon kafa na Yamai.

Har illah yau a jiya, Talata an yi karawa da tawagar kwallon kafa ta Najeriya data Afrika ta Kudu, inda suma suka tashin kunnen doki 0-0 

Yau Laraba akwai karawa tsakanin Mali da Burkina Faso, sai kuma karawa ta biyu tsakanin Ghana da Senegal.

A ranar Juma'a mai zuwa akwai karawa tsakanin Najeriya da Nijar mai masabkin baki.