Feb 04, 2019 05:29 UTC
  • AFCONU20 : Senegal Ta Lallasa Mali 2 - 0

A ci gaba da gasar cin kofin kwallon Afrika na 'yan kasa da shekara 20, dake gudana a Jamhuriyar Nijar, tawagar kwallon kafa ta Senegal, ta lallasa ta Mali da ci 2-0.

Yau Litini akwai karawa tsakanin Burkina Faso da Ghana.

Gobe Talata Najeriya zata yi karawarta ta biyu inda zata fafata da Afrika ta Kudu, sai kuma ita ma Nijar zata yi karawarta ta biyu inda zata fafata da Burindi.

A karawar farko ranar Asabar Nijar ta yi kunnen doki da Afrika ta kudu 1-1, sai kuma Najeriya wacce ta lallasa Burindi da 2-0. 

Tags