Feb 09, 2019 17:30 UTC
  • AFCONU20 : Najeriya Ta Yi Waje Da Nijar Mai Masabkin Baki

A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na 'yan kasa da shekara 20, dake gudana a Jamhuriyar Nijar, tawagar kwallon kafa ta Najeriya, ta yi waje da Nijar mai masabkin baki, bayan data doke ta da ci 1-0, a wasan da suka buga jiya Juma'a a Yamai.

Haka kuma a karawa ta biyu da akayi jiyan, Afrika ta kudu ta doke Burundi da ci 1 mai ban haushi.

Hakan dai ya sanya tawagogin kwallon kafa na Najeriya da Afrika ta Kudu, suka tsallake a wasa na gaba a rukunin A.

A wassanin da aka buga yau Asabar kuwa, tawagar kwallon kafa ta Senegal ta lallasa ta Burkina faso da 5-1.

Sai kuma karawa ta biyu da aka kammala dazu inda Mali ta doke Ghana da 1-0.

Tags