Pars Today
Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya na bukatar gyare-gyare a bangarori da dama.
Kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta'addancin da aka kai ranar Jumma'a a yankin kudu maso yammacin kasar Pakistan, harin da ya yi ajalin mutum 128 kana wasu 200 kuma suka jikkata.
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar amincewa da daftarin kudurin neman haramta sayar da makamai ga kasar Sudan ta Kudu.
Kasar Rasha ta hana kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya fitar da bayanin suka kan gwamnatin Siriya sakamakon rikicin yankin kudu maso yammacin kasar ta Siriya.
Mataimakin jakadan Amurka a majalisar dinkin Duniya Jonathan Cohen ya bukaci komitin tsaro na MDD ya dorawa JMI takunkumai don abinda ya kira sharrin Iran a yankin gabas ta tsakiya.
Babban Magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutress Ya ce wahalar da al'ummar Gaza suke sha tana nuni da kusantowar yaki
Jakadan kasar Rasha a kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya ce; Bayan da kasar Koriya ta Arewa ta bayyana shirinta na kawo karshen shirye-shiryenta na kera makaman nukiliya, to dole ne a kan kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya dauki matakin rage takunkumin da ya kakaba kan kasar ta Koriya.
Babban zauren Majalisar Dinkin Duniya ya zabi kasashen Jamus, Belgium, Afirka ta Kudu, Jamhuriyar Dominica da kuma Indonusiya a matsayin sabbin membobin Kwamitin Tsaro na Majalisar na wa'adin shekaru biyu.
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a zamansa a daren jiya Alhamis ya amince da karin wa'adin takunkumin da ya kakaba kan kasar Sudan ta Kudu.
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sake sabunta wa'adin aikin dakarun tabbatar da zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Afirka a kasar Somaliya.