Buhari: Kwamitin Tsaron MDD Na Bukatar Garambawul
(last modified Wed, 26 Sep 2018 06:55:16 GMT )
Sep 26, 2018 06:55 UTC
  • Buhari: Kwamitin Tsaron MDD Na Bukatar Garambawul

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya na bukatar gyare-gyare a bangarori da dama.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban babban taron majalisar dinkin duniya a daren Talata, inda ya ce ko shakka babu, yin gyara na adalci a cikin tsarin kwamitin tsaro zai amfani dukkanin al'ummomin duniya ne.

Haka nan kuma shugaba Buhari ya tabo batutuwa da suka shafi inganta harkokin tattalin arziki da tsaro da kuma kare hakkokin 'yan adam, kamar yadda ya tabo batun gudun hijira ba bisa ka'ida ba da kan jefa rayukan dubban daruruwan mutane a cikin hadari, da kuma muhimamncin inganta rayuwar jama'a domin kauce wa aukuwar irin wadannan matsaloli.

Tun a ranar Litin da ta gabata ce shugaba Buhari ya isa birnin New York na Amurka, domin halartar babban taron na majalisar dinkin duniya, wanda yake ci gaba da gudana a baban zauren majalisar da ke birnin na New York.