Dec 07, 2017 05:53
Kwamitin tsaron MDD zai gudanar da wani zama na gaggawa a gobe Juma'a don tattaunawa kan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump yayi na sanar da birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma shirin mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin na Qudus daga Tel Aviv.