MDD Ta Kara Yawan Dakarunta Da 900 A Afrika Ta Tsakiya
Kwamitin tsaro na MDD, ya amunce da gagarimin rinjaye da karin yawan dakarunsa da 900 da kuma tsawaita aikin tawagar da shekara guda a Jamhuriya Afrika ta Tsakiya.
Wannan dai bukata ce ta babban sakatare na MDD, Antonio Guterres , wanda ya yi kashedi kan kashe kashe masu nasaba da kisan kare dangi a wannnan kasa ta Jamhuriya Afrika ta Tsakiya.
A kudirin da kasashen mambobin kwamitin suka amunce da shi wanda kasar Faransa ta rubuta, tawagar wanzar da zaman lafiya a Afrika ta Tsakiya za ta kunshi dakaru 11,650 da suka hada da 'yan sanda 2,080 da kuyma sojoji masu sanya ido 480.
Jakadan Faransa a MDD, François Delattre, ya ce wannan kudirin na MDD zai taimaka matuka wajen shawo kan rikice-rikice da kuma samar da dawammanman zaman lafiya a AFrika ta Tsakiyar.
Amurka wacce tun da farko ta kudiri anniyar rage tallafin da atake bayarwa ga ayyukan tabbatar da zaman lafiya na MDD, ta ce bata adawa da karin dakarun na Minusca, amman da sharadin su nuna da gaske su ke a cikin aikinsu.