Matsayin Qudus : Kwamitin Tsaro Na MDD Ya Juyawa Amurka Baya
Kwamitin tsaro na MDD ya maida Amurka saniyar ware dangane da matakin shugaba Donald Trump na ayyana Qudus a matsayin babban birnin yahudawan sahayoniya 'yan mamaya na Isra'ila.
A taronsa na gaggawa dangane da batun a jiya Juma'a, kasashe mambobin kwamitin ciki har da kawayen Amurkar sun yi tir da kuma nuna matukar damuwarsu dangane da wannan matakin na Trump, wanda a cewarsu ya sabawa kudurorin kwamitin tsaro, sannan ba zai taba taimakawa ba wajen samar da zaman lafiya a yankin.
Jakadun kasashen turai biyar a kwamitin sun ce ba zasu taba amuncewa da wani mataki kan birnin Qudus ba, wanda ba'a samar ba ta hanyar sulhu, suna masu jadadda Qudus a matsayin babban birnin Palastinu da Isra'ila.
Kwamitin ya kuma yi matsin lamba wa Amurka akan ta gabatar da shawarwari dala-dala na magance rikicin bangarorin biyu.
Wannan dai ya kasance irinsa na farko da kwamitin tsaro ya maida Amurka saniyar ware akan wani kudiri da ka gabatar masa.
Da take maida martani a kwamitin tsaro, jakadiyar Amurka a MDD, Nikki Haley, ta ce Amurka ba ta bukatar ''wa'azi ko darasi'' tare da cewa lokacin yiwa Isra'ila rashin adalci a cikin kungiyar ya wuce.