Pars Today
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya mayar da martani kan rahoton Amurka na shekara-shekara kan kare hakkokin bil adama a kasashen duniya.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta mayar da martani dangane da sabbin takunkuman da gwamnatin kasar Amurka ta kakba wa kasar ta Iran.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Aljeriya ya bayyana hare-haren da Isra'ila take kaddamarwa kan yankin zirin Gaza da cewa ayyukan yaki ne a kan fararen hula marassa kariya.
Jami'an 'yan sandan kasar Somalia sun kaddamar da farmaki a kan babban ginin ma'aikatar harkokin wajen kasar da ke cikin birnin Magadishou fadar mulkin kasar, inda suka yi awon gaba da mataimakin ministan harkokin wajen kasar.
Gwamnatin kasar Iran ta yi allawadai da kisan kiyashin da jiragen yakin saudia da kawayenta suke ci gaba da yi a kasar Yemen.
Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, ya bayyana cewar Amurka za ta yi nadama mai girma matukar ta fice daga yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta yi kakkausar suka kan Kwamitin Kolin Kula da Kare Hakkin Bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya dangane da rahoton da ya fitar kan kasarta.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta rahotannin da ke cewa Iran din ta fara tattaunawa da wasu kasashen Turai dangane da irin tasirin da take da shi da kuma rawar da take takawa a yankin Gabas ta tsakiya.
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, ya bayyana cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba ja da baya komai kashinsa ba daga hakkin da take da shi na karfafa irin karfin kare kanta da take da shi ba.
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kakkausar suka da kuma Allah wadai da matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na mayar da ofishin jakadancin Amurka birnin Quds a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila yana tana mai cewa hakan wani lamari ne da zai kunna wutar sabon boren intifada a kasar Palastinun.