May 07, 2018 11:11 UTC

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran, Bahram Qassemi, ya bayyana cewar Amurka za ta yi nadama mai girma matukar ta fice daga yarjejeniyar nukiliyan da aka cimma da Iran.

Kamfanin dillancin labaran Hukumar Gidan Radio Da Talabijin na Iran ya bayyana cewar Kakakin ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya bayyana hakan ne a yau din nan Litinin a yayin da yake ganawa da manema labarai, inda yayin da yake magana kan barazanar Amurka na ficewa daga yarjejeniyar nukiliyan ya ce yarjejeniyar tana da nata matsayi na musamman wanda ficewa daga cikinta ba abu ne da za a amince da shi ba.

Kakakin Ma'aikatar harkokin wajen na Iran ya ce a halin yanzu dai Iran ta tsara dukkanin abubuwan da za ta yi matukar Amurka ta fice daga yarjejeniyar wanda ko shakka babu za ta yi nadamar ficewar.

Mr. Qassemi ya sake jaddada cewa Iran dai ba za ta zamanto mai fara karya yarjejeniyar ba, sai dai ba za ta taba amincewa da yin abin da zai sanya yarjejeniyar ta zamanto maras amfani a wajenta ba.

Tags