Pars Today
'Yan majalisar dokokin kasar ta Sudan sun yi sukar ne akan yadda gwamnati ta kasa warware matsalolin yau da kullum na rayuwar mutane
Kungiyar hadin kan majalisun kasashen larabawa ta sanar da cewa a gobe Alhamis za ta gudanar da wani taro na gaggawa a kasar Morocco don tattauna matsayar da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na sanar da birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Majalisar Dokokin Senegal ta kada kuri'ar amincewa da cire rigar kariya ga Khalifa Sall tsohon magajin garin birnin Dakar fadar mulkin kasar da yake matsayin dan majalisar a halin yanzu domin fuskantar shari'a.
Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Habasha ya yi murabus daga kan mukaminsa tare da bayyana shirinsa na fayyace dalilin yin murabus dinsa a nan gaba.
Rikici da doke-doke ya barke a majalisar dokokin kasar Uganda a kwana ta biyu tsakanin 'yan majalisar masu goyon bayan cire dokar da ta sanya iyaka ga shekarun dan takarar shugabancin kasar da kuma masu adawa da dokar.
Bayan kawo karshen aikin Majalisar dokokin Jamus da kuma bayyana sakamakon farko , Shugabar jam'iyyar Christian Democratic Union Angela Markel ta ce ba za su kafa gwamnati da jam'iyu masu adawa da manufar jam'iyar ba.
'Yan adawan kasar Afirka ta Kudu sun gabatar da wani kuduri na rusa majalisar kasar da gudanar da sabon zaben, 'yan kwanaki bayan kayen da suka sha a kokarin da suka yi na tsige shugaban kasar Jacob Zuma.
A jiya Jumma'a ce majalisar wakilan Nigeria ta fara bincike don gano yadda jandarmari na kasar Kamaru suka kashe yan Nigeria 97 a yankin bakasi daga kudu maso gabacin kasar.
Majalisar Dokokin Palasdinu ta bayyana cewa matakin da hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan palasdinawa ta dauka na hana 'yan Majalisar da suka fito daga kungiyar Hamas albashi yana matsayin shelanta yaki ne kan Majalisar.
shugaban majalisar wakilan kasar Masar Ali Abdul Ali, ne ya bada umarnin a bude binciken 'yan majalisar 5 da su ka halarci taron kunkiyar MKO mai fada da tsarin musulunci a Iran.