Majalisar Sudan Ta Soki Siyasar Tattalin Arziki Ta Gwamnatin Kasar
(last modified Thu, 11 Jan 2018 11:16:28 GMT )
Jan 11, 2018 11:16 UTC
  • Majalisar Sudan Ta Soki Siyasar Tattalin Arziki Ta Gwamnatin Kasar

'Yan majalisar dokokin kasar ta Sudan sun yi sukar ne akan yadda gwamnati ta kasa warware matsalolin yau da kullum na rayuwar mutane

Cibiyar watsa labaru ta al-Araby al-Jadeed ta ambato majiyar Majalisar a jiya laraba tana caccakar ma'aikatar kudi da sauran cibiyoyin gwamnati akan matsalar tattalin arzikin kasar da koma bayan kudin fam idan aka kwatanta shi da dalar Amurka.

A jiya laraba ne ministan kudi na kasar ta Sudan, Majdi Yasin, ya gurfana a gaban Majalisa inda ya fuskanci tambayoyi akan kasafin kudin shekarar bana 2018 da ya kunshi karin farashin wasu kayan masarufi na yau da kullum.

Tun ranar lahadin da ta gabata ne dai al'ummar Sudan suke gudanar da Zanga-zanga a cikin wasu birane saboda nuna kin amincewarsu da tsadar rayuwa.