Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Habasha Ya Yi Murabus Daga Kan Mukaminsa
Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Habasha ya yi murabus daga kan mukaminsa tare da bayyana shirinsa na fayyace dalilin yin murabus dinsa a nan gaba.
A zantawarsa da gidan talabijin na jihar Oromia na kasar Habasha: Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Habasha Abadula Gemeda ya sanar da cewa ya mika takardar yin murabus dinsa ga Majalisar Dokokin Kasar, kuma da zarar Majalisar Dokokin kasar da jam'iyyarsa sun amince da murabus din zai fito fili ya fayyace wa al'ummar kasar dalilinsa na yin murabus daga kanmukaminsa.
Wasu rahotonni suna bayyana cewa: Abadula Gemeda dan kabilar Oromia ne, kuma ya dauki matakin yin murabus daga kan mukaminsa ne domin nuna rashin amincewarsa da matakin da gwamnatin kasar take dauka na tursasawa kan al'ummar yankin Oromia da suke bore dangane da kwace musu gonaki da gwamnatin kasar ta yi.