Pars Today
Rahotanni daga Mali na cewa a kalla mutane 6 suka rasa rayukansu, a wani hari da aka kai a shelkwatar rundinar hadin gwiwa ta yaki da ta'addanci ta G5 Sahel, dake birnin Sevare a tsakiyar Mali.
Wata tawagar kungiyar kare hakkin bil'adama ta majalisar dinkin duniya ta tabbatar da cewa sojojin kasar Mali sun bindige har lahira wasu fararen hula a kan iyakar kasashen Mali da Borkina faso.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa kan yadda rikicin kabilancin da ya kunno kai a kasar Mali ya lashe rayukan fararen hula.
Shugaban hukumar kolin kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Wanzar da zaman lafiya da sulhu musamman a kasashen yankin Sahel zai taimaka wajen ragen kwararar 'yan gudun hijira zuwa kasashen Yammacin Turai.
Shugaban hukumar yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ya bukaci tallafin kudade don ganin an dawo da zaman lafiya a kasashen Mali, Niger da kuma Libya.
Wasu masu dauke da makamai da ba a tantance su ba, sun kai hari a kauyen Mopti da ke tsakiyar kasar Mali inda su ka kashe mutane 50
Rahotanni daga Mali na cewa a kalla fararen hula fulani 32 ne suka rasa rayukansu a wani hari da ake danganta wa dana mafarauta da ake kira ''Dozo'' a yankin.
Kungiyar kasa da kasa mai sa-ido akan tashe-tashen hankula( ICG) tq yi kira da a kawo karshen rikicin da yankin Sahel ke fama da shi ta hanyar tattaunawa
Ma'aitakar tsaro a Mali ta ce an kashe sojojinta uku da kuma jikkata wasu uku na daban a wani harin ta'addanci da aka kai kan wani sansanin soji da yankin Boni a tsakiyar kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta kan yadda rikicin siyasa ke ci gaba da yin kamari a kasar Mali tana mai jaddada yin kira ga gwamnatin Mali da 'yan adawar kasar da su dauki matakin sulhunta tsakaninsu.