Babban Sakataren MDD Ya Bayyana Damuwa Kan Rikicin Kabilancin Kasar Mali
(last modified Wed, 27 Jun 2018 12:32:03 GMT )
Jun 27, 2018 12:32 UTC
  • Babban Sakataren MDD Ya Bayyana Damuwa Kan Rikicin Kabilancin Kasar Mali

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa kan yadda rikicin kabilancin da ya kunno kai a kasar Mali ya lashe rayukan fararen hula.

A jawabin da babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya fitar kan rikicin kabilancin da ya kunno kai a kasar Mali ya bayyana tsananin damuwarsa kan yadda rikicin ya lashe rayukan mutane masu yawa tare da jaddada yin kira ga al'ummar kasar kan daukan matakin warware duk wani sabani da ya kunno kai a tsakaninsu ta hanyar lumana musamman gudanar da zaman tattaunawa a tsakaninsu.

Har ila yau Guterres ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda sojojin gwamnatin Mali suka aiwatar da kashe-kashe kan wasu shugabannin al'ummun kasar ba tare da gurfanar da su a gaban kotu ba domin hukunta su kan laifukan da suka aikata.

Rahotonni sun bayyana cewa: Mutane fiye da 50 ne da suka hada da kananan yara suka rasa rayukansu a yankin Mopti da ke tsakiyar kasar Mali bayan bullar rikicin kabilanci a 'yan watannin baya-bayan nan a yankin.