Pars Today
Sabanin mahanga tsakanin shugaban kasar Amurka da fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan kasar Siriya yana neman yin kamari.
Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya mayar wa firayi ministan Haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu da martani kan batun yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya.
Dariruwan mazauna birnin Tel-Aviv na HK Isra'ila sun taru a gaban gidan Firaminista Benjamin Netanyahu, inda suka nemi a gurfanar da shi a gaban shari'a saboda laifuka na cin hanci da rashawa da kuma zamba cikin aminci.
Ministan Tsaron Isra'ila ya kira taron gaggawa tare da halartar Gadi Eizenkot babban hafsan sojojin Isra'ila da wasu manyan janar janar domin tattauna yanayin da suke ciki da siriya.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana adawarsa da bayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar.
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah ya ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa za su debi kashinsu a hannun matukar gigi ya debe su suka kaddamar da yaki a kan kungiyar Hizbullah yana mai kiran yahudawan da suka yiyo hijira zuwa "Isra'ila" da su gaggauta komawa inda suka fito.
Wata kungiyar yahudawa masu tsatsauran ra'ayi ta kirayi sauran yahudawa domin su hada karfi da karfe domin kaddamar da farmaki a kan masallaci aqsa mai alfarma.
Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benyamin Netanyahu ya bayar da umarni ga jami'an tsaron yahudawan Isra'ila da su gaba da tsaurara bincike a kan Palastinawa a birnin Quds da kuma masallacin Aqsa mai alfarma.
Bayan gama ziyarar da ya kai a birnin Riyadh fadar masarautar Saudiyya, tare da gabatar da jawabi ga wasu shugabannin larabawa da na wasu kasashen musulmi, Donald Trump kai tsaye ya wuce zuwa Isra'ila.
Yahudawan kasar Mexico sun yi kakkausar suka da tofin Allah tsine ga firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu saboda goyon bayan shugaban kasar Amurka Donald Trump da yayi kan shirinsa na gina katanga tsakanin Amurka da Mexicon.