Macron Ya Bayyana Adawarsa Game Da Matakin Amurka Kan Birnin Qudus
(last modified Mon, 11 Dec 2017 06:16:56 GMT )
Dec 11, 2017 06:16 UTC
  • Macron Ya Bayyana Adawarsa Game Da Matakin Amurka Kan Birnin Qudus

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bayyana adawarsa da bayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya shawarci Firayi ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ke ziyarar aiki a kasar da ya yi taka tsantsan wajen daukar mataki kan rikicin yankin.

Macron ya ce akwai yiyuwar sake komawa teburin sulhu kan magance rikicin yankin in har an bi a hankali.  A jawabinsa  yayin ganawa da Neatanyahu, shugaba Macron ya soma da yin alla-wadai da rikicin da ya kunno kai a 'yan kwanakin nan a sanadiyar matakin shugaban Amurka Donald Trump kan mayar da Kudus babban birnin haramcecciyar kasar Isra'ila.

Shugaban ya jaddada wa Netanyahu kan daukar mataki na kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi a yankin Palastinawa, abin da ya ce zai kasance ginshiki a kokarin da ake yi na ganin an samar da zaman lafiya a yankin, Macron ya kara da cewa akwai bukatar yin nazari cikin tsanaki kan tatauna makomar yankin.

A nasa bangare Benjamin Netanyahu ya soki jamhuriyar musulinci ta Iran, inda yace manufar shigar Iran a kasashen Labnon, Siriya, Iraki, Yemen da zirin gaza, kawo karshen Isra'ila, kuma domin tabbatar da wannan manufa, ta fara shigar da dubban makamai masu lizzami cikin kasar Labnon.