Natenyahu Ya Jaddada Batun Rushen Kauyen Khanul-Ahmar Na Palasdinawa
Oct 22, 2018 07:48 UTC
Pira ministan na haramtacciyar Kasar Isra'ila ya fadi cewa; Ba za a dauki lokaci mai tsawo ba za a rushe kauyen na Khanul-Ahmar na Palasdinawa
Tuni dai 'yan sahayoniyar su ka girke manyan motocin rusau a kusa da kauyen na Palasdinawa wanda aka zagaye shi da gine-ginen matsugunan yahudawa 'yan share wuri zauna.
Bugu da kari, haramtacciyar kasar Isra'ilan tana son tilastawa Palasdinawa mazauna kauyen yin hijira zuwa wani wuri na daban.
Rushe kyauyen zai kawo karshen hanyar da ta hada yankunan Palasdinawa a yammacin gokin Jordan da birnin Kudus
Tags