Mar 19, 2019 16:35 UTC
  • Shugaban Kasar Kazakhstan,Ya Yi Murabus

Shugaban kasar Kazakhstan, Noursoultan Nazarbaïev, ya sanar da yin murabus daga mulkaminsa na shugaban kasar.

Da yake sanar da hakan a wani jawabi a gidan talabijin din kasar, shugaban kasar mai shekaru 78, ya ce ya dauki matakin yin murabus daga mukaminsa na shugaban kasa, saidai ba tare da yin wani karin bayyani ba kan dalilin yin hakan.

Saidai murabus din nasa na zuwa ne a kasa da wata guda, bayan rushewar ba zata da ya yi wa gwamnatinsa, dake zarginsa da gazawa akan farfado da tattalin arzikin kasar.

Mista Noursoultan, ya shafe shekaru kimanin talatin yana shugabancin wannan kasa ta Kazakhstan dake yankin Asiya ta tsakiya.

Kasar Kazakhstan, mai arzikin man fetur. ta jima tana fuskantar bore na jama'ar kasar saboda mastalar tattalin arziki.

Tags