Za A Kafa Dokar Hukunta Shugabannin Addinin Buda Masu Karbar Rashawa A Thailand
https://parstoday.ir/ha/news/world-i32271-za_a_kafa_dokar_hukunta_shugabannin_addinin_buda_masu_karbar_rashawa_a_thailand
Majalisar dokokin kasar Thailand ta kada kuri'ar amincewa da daftarin dokar hukunta jagororin addinin buda masu barnata dukiyar kasa.
(last modified 2018-08-22T07:02:05+00:00 )
Jul 10, 2018 12:48 UTC
  • Za A Kafa Dokar Hukunta Shugabannin Addinin Buda Masu Karbar Rashawa A Thailand

Majalisar dokokin kasar Thailand ta kada kuri'ar amincewa da daftarin dokar hukunta jagororin addinin buda masu barnata dukiyar kasa.

A zaman da majaisar dokokin kasar ta Thailand ta gudanar a jiya, ta kada kuri'ar amincewa da daftarin dokar hukunta jagororin addinin buda masu barnata dukiyar al'umma.

Jagororin addinin buda a kasar Thailand dai suna da matsayi na musamman, inda wasu daga cikinsu suke yin amfani da wannan damar cin karensu babu babbaka kan dukiyar kasar da sunan addini.

Dukkanin 'yan majalisar dokokin kasar su 217 ne suka amince da wannan daftarin doka, wanda zai bayar da damar hukunta jagororin addinin na buda kasar, wadanda ake kallon a matsayin suna a birbishin doka.