Pars Today
Rasha dake karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya 2018, ta lallasa Saudiyya da ci 5 da 0 a wasan bude gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya da aka yi a birnin Mosko.
An bude gasar kwallon kafa ta FIFA ta shekara ta 2018 a yau Ahamis a kasar Rasha, inda a taron da hukumar ta gudanar don zaben kasashen da zasu dauki nauyin gasar shekara ta 2026 suka kasashen Amurka Canada da kuma Mexico.
Shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad yayi watsi da wasu rahotanni da suke cewa akwai hannun kasar Rasha ko kuma tana da masaniyya kan hare-haren baya-bayan nan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kawo kasar kafin a kawo su.
Kasar Rasha, ta ce ba ta da wata niyyar komawa cikin kungiyar kasashe mafiya tattalin arzikin a duniya na G7, a halin yanzu.
Shugaban kasar Rasha ya yi furuci da cewa: Matakan da shugaban kasar Amurka ke dauka na bangare guda domin kare manufofin kasarsa yana kara haifar da matsaloli a tsakanin kasashen duniya.
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergueï Lavrov, ya gana da Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un a birnin Pyongyang, yau Alhamis a ci gaba da ziyarar da yake a kasar.
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa: Jami'an sojinta hudu da suke bada shawarwari kan dabarun yaki a kasar Siriya sun rasa rayukansu a lardin Dire-Zur da ke gabashin kasar Siriya.
Ministan wasanni da matasa na kasar Masar, Khalid Abd El-aziz, ya bayyana fatan cewa shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Mohammed Salah zai buga gasar kwallon kafa ta duniya da za gudanar a kasar Rasha duk kuwa da rauni da ya samu a kafadarsa a jiya Asabar.
Yayin da ranar fara wasan Cin Kofin kwallon kafa ta duniya ke kara kuratowa, an karfafa matakan tsaro, musaman a gariruwan da za su karbi bakuncin cin kofin kwallon kafa ta Duniya a kasar Rasha.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana amincewarsa da dalar Amurka 60 ya zama farashin danyen man fetur a kasuwannin duniya.