Rasha : Lavrov, Ya Gana Da Kim Jong Un, A Pyongyang
Ministan harkokin wajen Rasha, Sergueï Lavrov, ya gana da Shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jong Un a birnin Pyongyang, yau Alhamis a ci gaba da ziyarar da yake a kasar.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta fitar, ta ce Mista Lavrov ya je Koriya ta Arewar ne bisa goron gayyatar takwaransa, Ri Yong Ho, wanda shi ma ya ziyarci Rasha a watan Afrilu da ya gabata.
Bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa da kuma alakar dake tsakaninsu, inda har ma Rashar ta gayyaci Shugaba Kim Jong Un da ya ziyarci kasar.
Wannan ziyarar ta ministan harkokin wajen Rasha, na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirye shiryen ganawar da ake sa ran Shugabanin Amurka dana Koriya ta Arewar zasuyi a ranar 12 ga watan Yuni mai shirin kamawa.