Pars Today
Taho mu gama tsakanin dali'an jami'a da jami'an tsaron kasar Senegal ya yi sanadiyar mutuwar dalibi guda tare kuma da jikkata mutane 20 na daban.
Paparoma Francis na cocin Catholica ya bukaci a kawo karshen rikicin jamhoriyar Afirka ta Tsakiya.
Ma'aikatar tsaron kasar Tunusiya ta sanar da cewa dakarun sojin kasar sun yi arangama da 'yan wata kungiyar ta'addanci da ke gudanar da ayyukanta a yankuna masu duwatsu da ke yammacin kasar.
An Fara gudanar da zaben shugaban kasar Masar a kasashen ketare, kafin fara gudanar da zaben a cikin kasa.
Ma'aikatar lafiya a Libiya ta sanar da cewa: Akalla mutane 9 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu fiye da 30 suka samu raunuka a wani rikici da ya kunno kai a tsakanin kungiyoyi biyu masu dauke da makamai a kasar.
Shugaban kasar Tunisiya Beji Caid Essebsi ya tattaunawa dashugabanin jam'iyun siyasa da kungiyoyin fararen hula a wani mataki na kwantar da zanga-zangar adawa da tsarin gwamnati.
Shugaban kasar Sudan ya bayar da umarnin zartar da yarjejjeniyar tsagaita wuta a yankunan da ake rikici na tsahon watani uku.
Rikicin kabilanci ya lashe rayukan mutane akalla 22 a yankin Bor ta Kudu da ke jihar Jonglei na kasar Sudan ta Kudu.
Masu Zanga-zanga akan kin amincewa da hukuncin wata kotu a kasar na yanke hukuncin kisa ga matasa 6 ne suka yi taho mu gaba da jami'an tsaron kasar
Majiyar tsaron kasar Masar ta ce mutane 7 ne suka mutu a fadan da aka yi tsakanin sojojin kasar da kuma 'yan ta'adda a yankin al-Arish.