An Tsawaita Yarjejjeniyar Tsagaita Wuta A Yankunan Da Ake Rikici Na Sudan
Shugaban kasar Sudan ya bayar da umarnin zartar da yarjejjeniyar tsagaita wuta a yankunan da ake rikici na tsahon watani uku.
Wata majiya ta kusa da fadar shugaban kasar Sudan ta habarta cewa a wannan Alhamis Shugaban kasar Omar Al-bashir ya bayar da umarnin zartar da yarjejjeniyar sulhun da aka sabunta tsakanin gwamnati da kungiyoyin 'yan tawaye a yankunan da ake rikici har zuwa karshen watan Maris.
Rikici ya barke tsakanin Dakarun kasar sudan da kungiyoyin 'yan tawaye a yankunan Kordufan da Nile tun bayan da kasar Sudan ta kudu ta balle daga kasar ta Sudan.
Baya ga wadannan yankuna, tun a shekarar 2003 yankin Darfur dake yammacin kasar ta Sudan ya fama cikin rikici na kabilanci, biyo bayan zarkin da suka yi wa gwamnati da mayar da su saniyar ware, rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.