Paparoma Ya Bukaci A Kawo Karshen Rikici A Afirka Ta Tsakiya
(last modified Sun, 06 May 2018 19:09:58 GMT )
May 06, 2018 19:09 UTC
  • Paparoma Ya Bukaci A Kawo Karshen Rikici A Afirka Ta Tsakiya

Paparoma Francis na cocin Catholica ya bukaci a kawo karshen rikicin jamhoriyar Afirka ta Tsakiya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Paparoma Francis shugaban cocin Catholica ta Duniya, a yayin taron addu'o'i na cewa rikicin dake wakana a kasar Afirka ta tsakiya ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama, don haka ina bukatar dukkaninku ku yi wa al'ummar wannan kasar addu'a.

Har ila yau, Shugaban Cocin Catholica na Duniya ya bukaci da aka kawo karshen rikici, daukan fansa da kuma jubar da jin a fadin kasar gaba daya, sannan ya bukaci al'umma da su yi sulhu da kuma zaman lafiya a tsakaninsu.

Kasar Afirka ta tsakiya dai na daga cikin kasashen Duniya masu fama da talauci, sakamakon raunin gwamnatin kasar, kuma arzikin karkashin kasa kamar su zinari da Almas na daga cikin ababen dake haddasa rikici a kasar.