-
Rasha A Shirye Take Ta Tura Da Sojojin Kasanta Cikin Siriya Don Fada 'Yan Ta'adda
Apr 24, 2017 17:13Majiyoyin sojin kasar Siriya sun bayyana cewar Rasha ta sanar da gwamnatin kasar Siriya cewa a shirye take ta tura da sojojinta na kasa zuwa kasar Siriyan don taimakawa gwamnatin a fadar da take yi da 'yan ta'addan takfiriyya da suke samun goyon bayan kasashen waje.
-
Rauhani Wajen Bikin Ranar Sojoji: Iran Za Ta Mayar Da Martani Ga Masu Wuce Gona Da Iri
Apr 18, 2017 11:02Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bayyana cewar dakarun sojin Iran ba barazana ba ce ga kasashen makwabta da kuma yankin Gabas ta tsakiya, to amma za su mayar da martani mai kaushin gaske ga duk wanda yayi kokarin wuce gona da iri a kan Iran.
-
Yan Tawayen Sudan Sun Saki Sojojin Gwamnatin Kasar Da Dama Da Suka Kama
Mar 05, 2017 07:00Yan tawayen kungiyar Popular Movement for the Liberation of Sudan sun saki sojojin gwamnatin kasar da dama da suka kama a matsayin fursunonin yaki.
-
Adama Barrow Ya Sallami Babban Hafsan Hafsoshin Gambia
Feb 28, 2017 12:47Shugaban kasar ne Adama Barrow ya sallami babban hafsan hafsoshin sojin kasar Janar Ousman Badjie, tare da maye gurbinsa da Janar Masanneh Kinteh.
-
Gambiya: Shugaban Kasa ya Sauke Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Kasar Daga Mukaminsa.
Feb 28, 2017 08:07Majiyar Sojan Kasar ta Gambiya ta ce; Shugaban Kasar, Adama Barrow, ya sauke Usman Baji daga kan mukaminsa na hafsan hafsoshin sojojin kasar.
-
Rundunar Sojin Nijeriya Ta Sanar Da Gano Gawawwakin Sojojinta 16 Da Suka Bace
Jan 12, 2017 05:30Rundunar Sojin Nijeriya ta sanar da gano gawarwakin sojojinta 16 daga cikin 46 da aka sanar da bacewarsu sama da makonni shida da suka gabata a bakin rafin Yobe da ke arewa maso gabashin kasar.
-
Gambiya: Babban Hafasan Hafsoshin Sojan Kasar ya Nuna Goya Bayansa Ga Shugaba Jammeh
Jan 05, 2017 07:22Babban Hafsan hafsoshin sojan kasar Gambiya Usman Baji ya nuna cikakken goyon bayansa da na dukkanin sojojin kasar ga Shugaba Yahya Jammeh.
-
Nigeria Za Ta Tura Sojoji 800 Zuwa Darfur Don Aikin Tabbatar Da Zaman Lafiya
Jan 04, 2017 05:54Babban hafsan hafsoshin sojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya sanar da cewa Nijeriya za ta tura da sojoji 800 zuwa yankin Darfur na kasar Sudan don ci gaba da aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya.
-
Sojojin Burkina Faso 12 Sun Mutu Sakamakon Harin Da Aka Kai Wa Sansaninsu
Dec 16, 2016 17:12Rahotanni daga kasar Burkina Faso sun bayyana cewar wasu sojojin kasar su 12 sun rasa rayukansu sakamakon wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai wa wani sansaninsu da ke 'yankin Nassoumbou da ke lardin Soum da ke arewa masu yammacin kasar.
-
Sojojin Iran Sun Gwada Wani Sabon Jirgin Sama Mara Matuki Na Zamani
Dec 12, 2016 11:04A ci gaba da shirin Iran na ci gaba da kare kanta daga hare-haren makiya, sojojin kasar sun sanar da gwaji da kuma fara aikin wani sabon jirgin sama mara matuki na yaki da masanan kasar suka kera da aka ba shi sunan "Farpad".