Sojojin Iran Sun Gwada Wani Sabon Jirgin Sama Mara Matuki Na Zamani
(last modified Mon, 12 Dec 2016 11:04:15 GMT )
Dec 12, 2016 11:04 UTC
  • Sojojin Iran Sun Gwada Wani Sabon Jirgin Sama Mara Matuki Na Zamani

A ci gaba da shirin Iran na ci gaba da kare kanta daga hare-haren makiya, sojojin kasar sun sanar da gwaji da kuma fara aikin wani sabon jirgin sama mara matuki na yaki da masanan kasar suka kera da aka ba shi sunan "Farpad".

Kafar watsa labaran Tasnim na kasar Iran din ya bayyana cewar an gwada wannan sabon jirgin sama mara matukin ne a rana ta biyu ta atisayen da sojin kasa na Iran suke gudanarwa inda aka gwada irin ayyukan da jirgin yake yi.

Shi dai wannan jirgin wanda masana da kwararru na kasar Iran ne suka kera shi yana da karfin shawagi har na tsawon mintuna 45 ba tar da ya tsaya ba, kamar yadda kuma yake da karfin tattaro da kuma nadan bayanai bugu da kari kan tura su kai tsaye ga cibiyar da ke kula da shi kamar yadda kuma yake da karfi da gudun tsira ta yadda cikin sauki zai iya dawowa cibiyarsa a duk lokacin da ya fuskanci wata barazana daga wajen makiya.

A shekan jiya ne dai sojojin kasa na Iran din suka fara gudanar da wannan atisayen da aka ba shi sunan "Atisayen Muhammadu Rasulallah" don gwada wasu sabbin makamai da kuma dabarun yaki da sojojin suke da su.