Pars Today
Gwamnatin kasar Libiya ta sanar da sanya hannu kan yarjejjeniyar tsaro na kare iyakokin kasar da kasashen Nijar, Sudan da Chadi.
Shugaban kasar Sudan Umar Hassan El-Bashir ya bayyana matukar bacin ransa kan mummanan halin tattalin arzikin da kasarsa take ciki duk tare da cewa an dauke mata wasu takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata.
An Kai hari kan sansanin 'yan gudun hijra uku a yankin Darfur na yammacin Sudan tare da kashe 'yan gudun hijra dake ciki da kuma jikkata wasu na daban.
Cibiyar tsaron kasar Sudan ta hana wata tawagar 'yan jiridar kasar zuwa halattar zaman taro a kasar Saudiyya.
Gamayyar rundunar wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afrika a kasar Sudan ta yi gargadi kan sake bullar wani sabon rikici a yankin Darfur na kasar Sudan.
Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta kirayi jakadan Masar da ke kasarta domin bayyana masa rashin jin dadinta kan wani wasan kwaikwayo da za a nuna a wata tashar talabiji na kasar Masar.
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci karin tallafi domin agazawa 'yan gudun hijirar kasar Sudan sakamakon halin tsaka mai wuya da suke ciki.
Sabuwar hadin gwuiwan jam'iyyun adawa a kasar Sudan karkashin jagorancin Ghazi Salahuddin, shugaban jam'iyyar adawa ta Reform Now movement ta bukaci gwamnatin kasar da janye sojojin daga Yemen da kuma dawo da su gida.
Wata sabuwar gamayyar jam'iyyun siyasa ta kasar Sudan wacce ake kira "Gamayyar Hadin kan Kasa" ta bukaci gwamnatin kasar ta gaggauta dawoda sojojin kasar wadanda suke yaki a kasar Yemen.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa (Amnesty International), ta yi tir da matakin hukumomin Nijar na korar 'yan Sudan dake neman mafaka a kasar.