Jun 01, 2018 11:44 UTC
  • Shugaban Sudan Ya Bayyana Bacin Ransa Kan Mummuanan Halin Da Tattalin Arzikin Kasarsa Take Ciki

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan El-Bashir ya bayyana matukar bacin ransa kan mummanan halin tattalin arzikin da kasarsa take ciki duk tare da cewa an dauke mata wasu takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata.

Tashar talabijin ta al-jazira na kasar Qatar ta nakalto shugaban El-bashir yana fadar cewa duk tare da cewa an daukewa kasar wasu sassa na takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata yanayin tattalin arzikin kasar har yanzun yana nan kamar ba abinda ya sauya. 

Shugaban kasar ya kara da cewa kasar Sudan ta kasance cikin takunkuman tattalin arziki na tsawon shekaru 20, amma duk da cewa a halin yanzu an dauke mata wasu takunkuman amma ta kasa samun masu zuba jari a kasar daga cikin manya manyan cibiyoyin kudade na duniya. 

Daga karshe shugaban ya kammala da cewa , matsalolin siyasa na daga cikin abubuwan da suka haddasa mummunan halin da kasar take ciki a yanzu. Sai dai jam'iyyun adawar kasar sun dora laifin halin da kasar take ciki kan gwamnatin kasar . Tun farkon wannan shekara ta 2018 da muke cikin tashin farashin kayayyaki a kasar Sudan ya kai kashi 50%.

Tags