Pars Today
Zanga-zangar yin allawadai da tsadar rayuwa a kasar Sudan ta ci gaba kwanaki biyar a jere a yankuna daban-daban na kasar.
Kafar watsa labaru ta Alrakoba ta ce; Zanga-zangar da ake yi ta tilastawa gwamna jahar ta White Nile da iyalansa guduwa zuwa wani wuri da ba a san ko'ina ba ne
Madugun 'yan adawa a Sudan, Sadek al-Mahdi, ya bayyana cewa mutum 22 ne suka mutu a zanga zangar tsadar rayuwa data barke a baya bayan nan a wasu biranen kasar.
Gwamnatin kasar Sudan ta shelanta doka ta baci a kasar a dai-dai lokacinda zanga-zanga ta masu korafi kan tsadar rayuwa wanda ya hada da na abinci da bukatun yau da kullum yake kara bazuwa a kasar.
Rahotanni daga Sudan na cewa wasu akalla manyan jami'an biyar ne na jihar Gedaref, suka gamu da ajalinsu a yayin wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a gabashin kasar a iyaka da kasar Habasha.
Shugaban kasar Sudan ya jaddada bukatar kasarsa ta ganin an samu wanzuwar zaman lafiya da sulhu a dukkanin kasashen nahiyar Afrika.
Shugaban gamyar jam'iyun 'yan adawar Sudan na Nida'u Sudan ya bukaci gwamnati da ta yi aiki da dokokin tsarin milkin kasar domin fidda kasar daga matsalar da take ciki.
Jami'an kasar Sudan sun sanar da samun nasarar kwato wasu mutane 84 'yan kasashen waje ciki da har da mata 51 daga hannun 'yan wata kungiyar mai fataucin bil'adama a lardin Kassala da ke gabashin kasar.
Amurka ta ce a shirye take domin wajen aiwatar da shirin janye kasar Sudan daga cikin jerin kasashen dake goyan bayan ta'addanci.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta yi Allah wadai da aniyar shugaban kasar Amurka Donald Trump na shirin sake kara wa'adin takunkumin da Amurka ta kakaba kan kasar ta Sudan.