Pars Today
Kwamitin kare hakkin bil’adam na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi a gurfanar da jami’an tsaron gwamnatin kasar Sudan da ke da hannu a rikicin kasar na tsakanin shekara 2014 zuwa 2016.
Rahotanni daga kasar Sudan sun bayyana cewar Allah Ya yi wa tsohon shugaban kasar, Janar Abdulrahman Suwar Al-Dahab rasuwa yana dan shekaru 83 a duniya.
A jiya Alhamis ce majalisar dokokin kasar Sudan ta Kudu ta amince da yarjejeniyar sulhu wacce gwamnatin kasar ta cimma da yan tawaye kimanin wata guda da ya gabata.
Komitin tsaro na MDD ya tsawaita aikin dakarun tabbatar da zaman lafiya a kan iyakokin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu.
Gwamnatin kasar Sudan ta dauki matakin kara rage darajar kudin kasar, sakamakon matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar.
Wasu jiragen sama biyu ne su ka yi taho mu gama a filin saukar jirage na birnin Khartum wanda hakan ya kawo tsiko a zirga-zirgar jirage
Tashar talabiin din Skynews ta ambato kwamandan sojojin Somaliya Yufus Husain Usman na cewa;Sojojin wannan kasar sun kai farmaki a yankin Kismao inda su ka kwato wasu yankuna daga ikon kungiyar al-shabab.
Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun tattaunawa kan batun aiki tare na tabbatar da sulhu da kuma karfafa alaka tsakanin kasashen biyu
Wata kafar watsa labaran Sudan ta bayyana cewa: Barazanar da gwamnatin Amurka ta yi wa kotun kasa da kasa da ke shari'ar manyan laifuka a duniya lamari ne da ke fayyace Amurka a matsayar babbar mai take hakkin bil-Adama a duniya.
Rundunar sojin kasar Sudan ta sanar da mutuwar wasu sojojin kasar guda biyu a sakamakon faduwar wani jirgin yaki da suke ciki.