MDD Ta Nemi Gurfanar Da Omar al-Bashir A Kotun ICC
Nov 03, 2018 06:28 UTC
Kwamitin kare hakkin bil’adam na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi a gurfanar da jami’an tsaron gwamnatin kasar Sudan da ke da hannu a rikicin kasar na tsakanin shekara 2014 zuwa 2016.
Kwamitin ya ce akwai bukatar gwamnatin Sudan ta bada hadin kai ga kotun ta ICC wadda ta bukaci a kamo mata Shugaba Omar Al-Bashir saboda zargin laifukan yaki.
Dubban mutane ne dai aka kashe a yakin kasar ta Sudan, da kuma yankin yammacin Darfur a fafatawar da akayi tsakanin ‘yan tawaye da Sojojin gwamnati, lokacin da gwamnatin ta kara waadin dokar ta baci.
Shugaban ksar ta Sudan dai Omar al-Bashir na ci gaba da musanta hannunsa a laifukan yakin da ake zarginsa.
Tags