Sudan: An Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Sama A Khartum
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33466-sudan_an_dakatar_da_zirga_zirgar_jiragen_sama_a_khartum
Wasu jiragen sama biyu ne su ka yi taho mu gama a filin saukar jirage na birnin Khartum wanda hakan ya kawo tsiko a zirga-zirgar jirage
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Oct 04, 2018 08:03 UTC
  • Sudan: An Dakatar Da Zirga-zirgar Jiragen Sama A Khartum

Wasu jiragen sama biyu ne su ka yi taho mu gama a filin saukar jirage na birnin Khartum wanda hakan ya kawo tsiko a zirga-zirgar jirage

Kafar watsa labaru ta Sudan Tribune ta ce jiragen da su ka yi karo da juna su ne nau'in Antonov AN30 da An32.

Jiragen biyu sun sauka ne akan titi daya kusa da kusa abin da ya kai ga yin karo a tsakaninsu. Mutane takwas ne aka tabbatar da cewa sun jikkata sanadiyyar abin da ya faru.

Jami'an filin saukar jiragen sama na Sudan ta sanar da ta dakatar da tashi da saukar jiragen sama a filin.

A cikin watanni biyu da su ka gabata, an sami irin wannan hatsarin har sau uku a filin saukar jiragen saman na birnin Khartum.

A cikin watan Satumba na wannan shekarar wani jirgin saman ya fadi a yankin Wadi Sayyidina a arewacin birnin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar matukan jirgin.