Sudan Ta Kara Rage Darajar Kudin Kasarta
Gwamnatin kasar Sudan ta dauki matakin kara rage darajar kudin kasar, sakamakon matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin Sudan ta rage darajar kudin kasar da kimanin kashi 60% tun daga farkon wannan shekara.
Ana sayar kudin Junaih 28 ne a kan dala daya, amma sai babban bankin kasar ya mayar da shi Junaih 45.5 a kan dala daya, a jiya Lahadi kuma babban bankin an Sudan ya kara karya darajar kudin na Junaih zuwa junaih 47.5 a kan kowace dala daya ta Amurka.
Daya daga cikin mambobin kwamitin kula da harkokin tattalin arzikin kasar ta Sudan Abbas Abdullah ya bayyana cewa daukar wannan mataki ya zama wajibi, matukar ana son a rage yawan matsalolin da ake fuskantar na rashin kudade a hannun gwamnati.