Pars Today
Sabuwar gwamnatin kasar Sudan karkashin firaiminista Mutaz Musa Abdullahi ta yi rantsuwar kama aiki, a dai-dai lokacinda kasar take cikin tsananin matsalolin tattalin arziki.
Sabuwar gwamnatin Sudan ta yi rantsuwar kama aiki da nufin fuskantar tarin matsaloli da suke ci gaba da addabar kasar musamman matsalar tattalin arziki.
Mataimakin Shugaban kasar Sudan ya sanar da kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa mai kumshe da ministoci 21 da mashawartan ministoci 27 a kasar
Kasashen Masar da Sudan sun cimma wata muhimmiyar yarjejeniya kan sabanin da ke tsakaninsu dangane da ruwan tekun maliya da ya ratsa kasashensu.
Wasu daga cikin sojojin Sudan da suke yaki karkashin rundunar kawancen Saudiyya a kasar Yamen sun fara komawa gida sakamakon matsin lamba da suke fuskanta.
Shugaba Omar Al-Bashir na kasar Sudan ya yi da'awar cewa rage jami'an Diplamasiyar kasar da ya yi a kasashen waje zai taimaka wajen rage kudaden da kasar ke kashewa.
Al'ummar Sudan tana ci gaba da sanya matakin matsin lamba kan gwamnatin kasar kan daukan matakin janye sojojin kasar daga rundunar kawancen Saudiyya da ke yaki a kasar Yamen.
A wani zaben jin ra'ayin da aka gudanar a kasar sudan sakamakon ya nuna cewa kashi 92% na mutanen kasar basa goyon bayan shugaba Umar Hassan Al-Bashir ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben shekara ta 2020.
Babban hafasan hafsoshin sojojin Sudan Kamal Abdul Ma'aruf ne ya sanar da haka a yayin ganawa da takwaransa na kasar Habasha Ma'ara Makonan
A wani rahoton da majalisar dinkin duniya ta fitar, an bayyana cewa mayakan 'yan tawayen yankin darfur na kasar Sudan na karuwa a kasar Libya.