Kashi 92% Na Mutanen Sudan Basa Goyon Bayan Shugabancin Al-Bashir.
(last modified Sat, 18 Aug 2018 06:29:31 GMT )
Aug 18, 2018 06:29 UTC
  • Kashi 92% Na Mutanen Sudan Basa Goyon Bayan Shugabancin Al-Bashir.

A wani zaben jin ra'ayin da aka gudanar a kasar sudan sakamakon ya nuna cewa kashi 92% na mutanen kasar basa goyon bayan shugaba Umar Hassan Al-Bashir ya sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben shekara ta 2020.

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto wata kungiya ta masu kishin kasar sudan wacce ta bayyana cewa ta gudanar da zaben jin ra'ayin jama'ar kasar a shafukan sadarwan dangane da sake tsayawa takarar shugaban kasa na shugaba Umar Hassan Albashir a zaben shekara ta 2020, inda mutanen dubu 67900 suka bayyana ra'ayinsu. sannan kashi 92% wato mutum dubu 62 kenan suka bayyan ra'ayin kin hakan a yayinda kashi 8% kuma suka amince. 

Shugaban Umar Hassan Al-bashir dai yana mulkin kasar Sudan tun shekara ta 1993 . Sai dai duk da cewa kundin tsarin mulkin kasar ta yanzun ta amince masa shugabancin kasar ne kawai zuwa shekara ta 2020, amma tuni jam'iyya mai mulkin kasar ta amince masa shiga takarar shugabancin kasar a zaben na shekara ta 2020.