Sabuwar Gwamnatin Sudan Ta Yi Rantsuwar Kama Aiki
Sabuwar gwamnatin Sudan ta yi rantsuwar kama aiki da nufin fuskantar tarin matsaloli da suke ci gaba da addabar kasar musamman matsalar tattalin arziki.
Tashar Sky News ta watsa rahoton cewa: Sabuwar gwamnatin Sudan karkashin jagorancin fira minista Mu'utaz Musa Abdullahi mai kunshe da ministoci 21 da kuma kananan ministoci 27 ta yi rantsuwar kama aiki da nufin daukan kwararan matakai domin shawo kan tarin matsalolin da kasar ta shiga musamman a harkar tattalin arziki.
Faisal Hassan Ibrahim mataimakin shugaban kasar Sudan ya bayyana cewa: A sabuwar gwamnatin Sudan an dauki matakin rage yawan ministoci daga 31 zuwa 21 tare da barin ma'aikatar kudin kasar a hannun sabon fira ministan da nufin kokarin farfado da harkar tattalin arzikin kasar.
A cikin 'yan shekarun baya-bayan nan kasar Sudan ta shiga cikin kangin matsalar tattalin arziki da fuskantar karancin kudaden waje lamarin da ya kara janyo tsadar rayuwa musamman farashin kayayyakin bukatu na yau da kullum.