Kasashen Sudan Da Habasha Za Su Girke Sojojin Hadin Gwiwa Akan Iyakokinsu
(last modified Fri, 17 Aug 2018 19:03:42 GMT )
Aug 17, 2018 19:03 UTC
  • Kasashen Sudan Da Habasha Za Su Girke Sojojin Hadin Gwiwa Akan Iyakokinsu

Babban hafasan hafsoshin sojojin Sudan Kamal Abdul Ma'aruf ne ya sanar da haka a yayin ganawa da takwaransa na kasar Habasha Ma'ara Makonan

A yayin ganawar Abdul ma'aruf ya ce; Ganawar tasu tana a karkashin aikin da kasashen biyu suke yi tare ne domin fada da ayyukan ta'addanci.

Jami'in Sojan na Kasar Sudan ya kuma ba da labarin cewa kasashen biyu sun kafa wani kwamiti wanda zai yi nazarin hanyoyin da za a warware sabanin da ake da shi akan tsaron iyakoki.

A nashi gefen, babban hafsan hafsoshin sojan kasar Habasha, ya jaddada cewa kasarsa tare da Sudan sun amince da su girke sojoji na hadin gwiwa akan iyaka domin tabbatar da tsaro da kalubalantar barazanar ta'addanci