An Shelanta Dokar Ta Baci A Sudan Saboda Karin Tashe-Tashen Hankula
Gwamnatin kasar Sudan ta shelanta doka ta baci a kasar a dai-dai lokacinda zanga-zanga ta masu korafi kan tsadar rayuwa wanda ya hada da na abinci da bukatun yau da kullum yake kara bazuwa a kasar.
Shafin yanar gizo na Sudan ya bayyana cewa gwamnatin kasar Sudan ta dauki wannan matakin ne bayan da zanga-zanga ta tsadar rayuwa yake yaduwa a yankuna da dama na kasar.
Labarin ya kara da cewa a birnin Atbara da kuma Port Sudan inda shugaban kasar ta Sudan Umar Hassan El-Bashir yake halattar atisai na jiragen yaki, mutane zun fito zanga-zanga don nuna matsin da suke ciki saboda tsadar abinci da kayakin bukatun yau da kullum.
Komitin tsaro na birnin Atbara ta shelanta doka hana fita daga 6 na safe zuwa 6 na yamma, sannan sun rufe dukkan makarantu a birnin sai abinda hali yayi.
A jiya Laraba masu zanga-zanga sun kona ofishin jam'iyya mai mulkin kasar a birnin Atraba, sun kuma buka ce gwamnati ta yi murabus.
A birnin Khartum babban birnin kasar ma, mazu zanga-zanga sun yi ta kota tsoffin tayoyi da kuma rare taken "ba yunwa ba tsada".
Wasu labarai sun bayyana cewa an fara samun karancin makamashi a wasu yankuna a kasar ta Sudan a cikin yan kwanakin da suka gabata.