Pars Today
Ofishin bayar da agajin gaggauwa na MDD ya bayyana damuwarsa game da awan gaba na ma'aikatansa shida a kasar Sudan ta Kudu.
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi bangarorin da suke rikici da juna a kasar Sudan ta Kudu da su nisanci ci gaba da kunna wutan rikici a yankin.
Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Silva Kiir ne ya sanar da kafa dokar ta baci a jahohi ukun domin kwance damarar yaki a cikinsu.
Mahukuntan Sudan ta Kudu sun sanar da cewa: Rikicin kabilanci tsakanin makiyaya ya lashe rayukan mutane akalla 170 a yankin da ke tsakiyar kasar.
Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto majiyar gwamnatin kasar ta Sudan ta kudu na cewa Mutane 60 ne suka mutu da kuma jikkata.
Rahotanni daga Sudan ta Kudu na cewa a kalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 19 na daban suka raunana a wani rikicin kabilanci a jihar Jonglei dake gabashin kasar.
Wani komandan sojojin kasar Sudan ta Kudu mai suna Zakariyya Munjik faqut ya bayyana ballewarsa daga sojojin gwamnati da kuma kafa wata sabuwar kungiyar yan tawaye don kubutar da kasar daga hannun shugaba Silva Kirr.
Kakakin gwamnatin Sudan ta Kudu ya sanar da cewa: Gwamnatin kasar ta kara wa'adin dokar ta baci a wasu lardunan kasar.
Shugabannin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu, sun yi alkawarin cewa ba za su mara baya ko ba da mafaka ga kungiyoyin dake adawa da gwamnatocin su ba.
Hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a jiya alhamis cewa; A cikin watannin bayan nan yan sanda a Khatum sun tilastawa yan gudun hijirar komawa zuwa wani wuri na daban.