Rikicin Kabilanci Ya Yi Ajalin Mutum 40 A Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25875-rikicin_kabilanci_ya_yi_ajalin_mutum_40_a_sudan_ta_kudu
Rahotanni daga Sudan ta Kudu na cewa a kalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 19 na daban suka raunana a wani rikicin kabilanci a jihar Jonglei dake gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:31:04+00:00 )
Nov 29, 2017 17:35 UTC
  • Rikicin Kabilanci Ya Yi Ajalin Mutum 40 A Sudan Ta Kudu

Rahotanni daga Sudan ta Kudu na cewa a kalla mutane 40 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 19 na daban suka raunana a wani rikicin kabilanci a jihar Jonglei dake gabashin kasar.

Ministan yada labarai na kasar, Jacob Akech Dengdit, ya shidawa kamfanin dilancin labaren Xinhua cewa maharan sun fito ne daga yankin Boma inda suka faramawa kauyuka suka kuma kashe mutane kimanin 40 da yin awan gaba da mata da yara.

ko baya ga hakan a cewar ministan maharan sun kona gidajen jama'a a kauyukan biyu da suka hada da Duk Panyang da Duk Payuel tare kuma da yin awan gaba da dabbobi 

Kafin rikicin dai shuwagabbin kabilun yankunan dake makofataka da juna sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta kawo karshen rikice rikice dake janyo hasara rayukan mutane tsakaninsu.

Ko a karshen shekara 2016 data gabata,rikici makamancin wannan a yankin ya yi ajalin mutane hamsin.