Pars Today
Majiyar rundunar 'yan sandan Kenya ta sanar da cewa: 'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan al'ummar garin Lokichogia da ke shiyar arewa maso yammacin kasar Kenya.
Kungiyar bada agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta sanar da cewa: Ma'aikatanta sun koma bakin aikinsu a yankunan da suke yammacin kasar Sudan ta Kudu.
Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta bada sanarwan cewa sojojinta sun kashe yan tawaye 91 sannan wasu da dama sun ji rauni a fadan baya bayan nan
Dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawayen kasar ya lashe rayukan mutane fiye da 25 a shiyar arewacin kasar.
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu, ta sanar da janye ma'aikatan agajinta 30 daga yankin Aburoc dake jihar Nil saboda barkewar wani rikici.
Kungiyar kai agajin gaggawa ta kasa da kasa ta sanar da kisan jami'inta a kasar sudan ta kudu
Majiyar yan tawayen kasar Sudan ta Kudu ta bayyana cewa, dakarunsu sun dawo da ikonsu kan garin Pagak daga hannun sojojin gwamnati kwana guda bayan sun koresu daga garin.
Sojojin kasar Sudan ta Kudu sun kwace babban sansanin 'yan tawayen kasar na Pagak da ke kan iyakan kasar da kasar Ethiopia, lamarin da ya sanya dubun dubatan mutanen gudu da barin wajen.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Amnesty" ta yi gargadi akan ci gaba da cin zarafin mata da ake yi a kasar Sudan ta Kudu
Jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu ya jaddada cewa: Dole ne gwamnatin Sudan ta Kudu da bangaren 'yan tawayen kasar su hanzarta samar da wata hanyar wanzar da zaman lafiya da sulhu a tsakaninsu.