MDD Ta Nuna Damuwarta Kan Rikicin Kasar Sudan Ta Kudu
(last modified Fri, 21 Jul 2017 18:49:49 GMT )
Jul 21, 2017 18:49 UTC
  • MDD Ta Nuna Damuwarta Kan Rikicin Kasar Sudan Ta Kudu

Jami'in Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu ya jaddada cewa: Dole ne gwamnatin Sudan ta Kudu da bangaren 'yan tawayen kasar su hanzarta samar da wata hanyar wanzar da zaman lafiya da sulhu a tsakaninsu.

A jawabinsa a gaban kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a yau Juma'a: Qasim Wayne mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Sudan ta Kudu ya yi furuci da cewa: Shirin wanzar da zaman lafiya da sulhu a Sudan ta Kudu suna fuskantar matsaloli masu tarin yawa, don haka dole ne a kan bangaren gwamnatin kasar da na 'yan tawaye sun sake komawa kan teburin tattaunawa da nufin samar da hanyar warware rikicin da ke tsakaninsu.

Har ila yau Qasim Wayne ya bayyana takaicinsa kan yadda ake ci gaba da samun bullar tabarbarewar matakan tsaro a kasar, kamar yadda tuni dukkanin bangarorin da basu ga maciji da juna a kasar suka yi watsi da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a tsakaninsu.