An Kashe Mayakan Yan Tawaye Masu Yawa A Sudan Ta Kudu
(last modified Tue, 03 Oct 2017 06:45:52 GMT )
Oct 03, 2017 06:45 UTC
  • An Kashe Mayakan Yan Tawaye Masu Yawa A Sudan Ta Kudu

Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta bada sanarwan cewa sojojinta sun kashe yan tawaye 91 sannan wasu da dama sun ji rauni a fadan baya bayan nan

Kamfanin dillancin labaran Xinhua na kasar China ya nakalto kakakin sojojin kasar Lul Ruai Koang yana fadar haka a jiya Litinin ya kuma kara da cewa kafin haka yan tawayen sun kashe sojojin gwamnati guda 4 a ranar Lahadi, wanda ya sa sojojin kasar suka mai da martani suka kuma kashe akalla mayakan yan tawaye 91.

Mai magana da yawun sojojin kasar sudan ta kudu ya kara da cewa mayakan yan tawayen suna son samarwa bangarensu karin matsayi ne a tattaunawan sulhun da ke gudana a halin yanzu.

An fara yakin basasa a kasar Sudan ta kudu ne tun watan Decemban shekara ta 2013 bayan da shugaba Silver Kirr ya kori mataimakinsa Riek Macher daga mukaminsa