Hadarin Helikoftan MDD, Ya Yi Ajalin Mutum 3 A Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35158-hadarin_helikoftan_mdd_ya_yi_ajalin_mutum_3_a_sudan_ta_kudu
Wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar dinkin duniya ya yi sanadiyar mutum uku da kuma raunata wasu 10 a Sudan ta Kudu.
(last modified 2019-02-10T09:47:11+00:00 )
Feb 10, 2019 09:47 UTC
  • Hadarin Helikoftan MDD, Ya Yi Ajalin Mutum 3 A Sudan Ta Kudu

Wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar dinkin duniya ya yi sanadiyar mutum uku da kuma raunata wasu 10 a Sudan ta Kudu.

Sanarwar da MDD, ta fitar ta ce jirgin ya fadi ne a wani sansaninta dake jihar Abiye, inda mutum uku suka mutu kana wasu goma suka raunana, ciki harda uku da suka samu munanen raunuka.

Jirgin kirar MI-8 na dauke fasinjoji 23 a lokacin da ya yi hadarin.

Kwamandan riko na rundinar tsaron MDD, (FISNUA) a yankin, Janar Gebre Adhana Woldezgu., ya ce ana gudanar da bincike kan lamarin.