Sudan Ta Kudu Zata Dakatar Da Amfani Da Yara A Yaki
Gwamnatin kasar Sudan ta kudu ta bada sanarwan cewa zata kawo karshen amfani da yara a matsayin sojoji a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xinhua na kasar Cana ya nakalto ministan tsaron kasar ta Sudan ta Kudu yana fadar haka a wani bayanin da ya fitar a jiya Laraba.
Bayanin ya kara da cewa gwamnatin kasar ta bada umurni ga dukkan komandojojin sojojin kasar da kada su sake amfani da yara a cikin yake-yaken da suke yi da yan tawaye a kasar.
A shekarar da ta gabata, wato 2018 ne gwamnatin Sudan ta Kudu ta rattaba hannu kan wata yerjejeniyar ta rashin amfani da yara a yaki.
Sannan hukumar kare yara ta MDD , UNICEF ta bada sanarwan cewa a cikin shekaru 5 da suka gabata gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta sallafi yara kimani 3,100 daga ayyukan soje.
Kasar Sudan ta kudu dai ta fada cikin yakin basasa a shekara ta 2013 inda ya zuwa yanzu dukkan mutanen kasar suka mutu, sannan wasu miliyoyi kuma suka zama yan gudun hijira.