Jan 01, 2019 06:48 UTC
  • Yawan Yan Gudan Hijira Ya Karu A Shekarar Da Ta Gabata A Duniya.

Hukumar yan gudun hijira ta MDD ta bada sanarwan cewa yawan yan gudun hijira a duk fadin duniya ya karu a cikin shekarar da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya bayyana cewa hukumar yan gudun hijirar ta bayyana haka ne a rahotonta na shekara-shekara kan yan gudun hijira a duniya . Ta Kuma kara da cewa a halin yanzu akwai yan gudun hijira kimani miliyon 68, da dubu 500 wadanda suka akuracewa gidanjensu.

Hukumar ta kara da cewa shekarar da ta gabata, shekara ce mai tsanani ga hukumar da kuma yan gudun hijira don ta kasa samun tallafin da take bukata don kula da yan gudun hijira a kasashen duniya daban daban 

Dangane da kasar Yemen, Hukumar ta bayyana cewa akwai mutane kimani miliyon 20 a kasar Yemen wadanda suke bukatar abinci da gaggawa saboda killace kasar da kuma fari. 

A kasar Sudan kuma Hukumar ta ce akwai yan gudun hijira miliyon 2. dubu 200 wadanda suke gudun hijira.

Tags